8.11.07

MAFARKIN SHABBAKIN MANZON ALLAH SAWA

KIN MANZON SALAM.
Bayan haka ina yiwa al'ummar musulmi masoya Manzo Muhammad SAWA da Iyalansa tsarkaka a duk inda suke a duniya fatan alheri, musamman 'yan uwana 'yan darikar Tijjaniyya ta Maulanmu Shehu Ahmad Tijjani RTA da kuma masoyanmu masu kaunarmu a duk inda suke.
Bayan haka yau Litinin 26-10-1428 (5-11-2007) da daddare da misalin karfe 2:00 na dare ina barci sai nayi mafarki da Shabbakin Manzon Allah SAWA da yake garin Madina, inda na ganni a bakin Shabbakin a tsaye wasu mutane fararen fata suna zuwa domin suyi ziyara ga Manzon Allah SAWA ana korarsu idan suna yin addu'o'i a wajen, inda shi mai kula da wajen wanda bakar fata ne kuma yana magana da harshen Hausa, yake nuna mini wadannan mutane suna yin wani abu ne mara kyau, a halin ba abin da suke yi sai tawassilli da Manzon Allah SAWA. A lokacin dana kusancin makwancin Manzon Allah SAWA sai na leka ta wata kofa inda naga Kabarinsa mai albarka da kwarjini, sannan a gefen kabarin akwai wasu kabararruka kana guda uku wanda basu kai na Manzon Allah SAWA girma ba, su wadannan kananan kabararruka sai na ga shi wannan mutumi mai kula da wajen yana diban wasu sarkoki na gwalagwalai yana yi musu ado da su amma bai kula da na Manzon Rahama SAWA ba. A lokacin da nake leka kabarin Manzon Allah SAWA ta cikin wasu kananan kofofi sai nake fadin,"ASSALATU WASSALAMU ALAIKA YA MUHAMMADUR RASULILLAH ! ASSALATU WASSALAMU ALAIKA YA ABUL FATIMA ZAHARA'U ! ASSALATU WASSALAMU ALAIKA YA ABUL KASIM ! ASSALATU WASSALAMU ALAIKA YA ABUL ZAINAB ! ASSALATU WASSALAMU ALAIKA YA ABUL UMMUL KULSUM!..... ......... ."
Haka na ganni ina ta yiwa Manzon Allah SAWA kirari da salati, har sai dana ga kabarinsa yana dada girma yana yin numfashi kamar kabarin zai bude ya fito. A lokacin da wannan mai kula da kabarin ya ga halin da nake ciki wanda har na fita daga hayyacina saboda kirarin da salati da nake yi masa SAWA a gaban kabarinsa SAWA, sai wannan mai kula da waje ya kama ni ya damkawa wani askari ni, wato sojan kasar Saudiya, wanda shi kuma ya rike hannayena guda biyu ya tafi dani wajen shugabansa wanda shi kuma ya umarce shi daya kai ni wani waje da suke azabtar da mutane. A lokacin sai wannan soja yake duka na da wani abu mai kama da bindiga, amma sai nake ji kamar yana shafata da wani abu mai tsananin taushi banji alamar wani ciwo ko zafi ba.
A lokacin da wannan askari yake kokarin tafiya dani sai nake masa magana da harshen turanci al'amarin daya jawo dimbin jama'ar da suke zaune a cikin masallacin suka saurari tambayar da nake yiwa wannan askari, kuma suka zaku su ji tambayar da nake yi masa da amsar da zai bani.
Na tambayi wannan askarin cikin harshen turanci shin bani da iko in bi mazahabar da nake ganin itace ta dace na bita, kuma na aiwatar da ayyukan ibadata daidai da fahimta ta?
A lokacin da nake tambayar wannan askarin sai yake kokarin ya hana ni karasa tambayata saboda ya hana mutane su fahimci wane ne mai gaskiya a tsakani na da shi, inda yake fada mini wai limaminsu Sudais ma'asumi ne don haka kawai in bi hanyar limamansu.
A lokacin da wannan askari ya gaza hana jama'a fahimtar abin da nake son fada har jama'a suka fahimci abin da yake faruwa sai kawai naga jama'a bakaken fata da suke wajen wanda akasarinsu talakawa ne masu kananan sana'o'i irin sai da lemon zaki, sun watsar da kayan sana'arsu sun nufo inda nake, suma mata wanda na gansu cikin shiga irin ta matan 'yan uwa musulmi almajiran Malam Zakzaky sanye da hijabi wanda suma suka baro wajen da suke a zaune a masallacin suka nufo inda nake inda na gansu dubunnai suna fadin, "ASSALATU WASSALAMU ALAIKA YA MUHAMMADUR RASULILLAH ! ASSALATU WASSALAMU ALAIKA YA MUHAMMADUR RASULILLAH !!"
Wannan askar da sauran 'yan uwansa suna ganin yadda mutanen nan suka kawo mini tallafi sai ya sake ni ya nemi sulhu dani.

Wannan shine mafarkina wanda nayi kuma dama wani abu makamancin haka ya taba faruwa da ni a lokacin dana je aikin Hajji a shekarar 2000.
Allah ya kara mana son Manzon Allah SAWA da Iyalansa tsarkaka da masoyansu ko da kuwa muna da bambamcin fahimta dasu matukar dai su masoyan Manzon Manzon Allah SAWA ne da Iyalansa tsarkaka.
Wannan mafarki nawa yana dauke da babban sako ga mai hankali.
Daga,
Rabiu Yusuf Kano,

No comments: