8.11.07

SUN FI SU

A sakamakon mukalar dana aikowa da mujallar Fim mai farin jini wadda na bayyana cewa 'yan fim sun fi malamai masu kasuwanci da ayoyin Allah SWT fadakarwa wadda mujallar fim ta buga, na samu kiran waya da sakonni daga jihohi da dama da suke kasar nan ta (Najeriya). Babu lokacin da zan bayyana irin sakonnin dana samu daga wajen Malamai da matasa sai dai in ce lalle ina kara jaddada maganata cewa 'Yan Fim sun fi Malamai Fadakarwa amma fa Malamai masu boye gaskiya suna bayyana karya da son zukatansu, Malamai masu kafirta al'ummar Muhammadu Rasulillahi SAWA saboda kawai ba sa bin abin da suke so na zalunci da son zukatansu.
Shin mai yiwa Allah SWT da Manzonsa SAWA karya ne yafi zalunci ko kuwa wanda yake rawa da matar da bata sa ba? Kuma al'umma kun san wanda ya kirkiri karya ya jinginawa Allah SWT da Manzonsa SAWA don biyan bukatarsa kansa ko bukatar ubangidansa yafi zalunci akan wanda ya ke rawa da waka da matar da ba muharramar sa ba.
Ina so al'umma ta fahimci sai bango ya tsage kadangare yake samun wajen shiga ya fake, ma'ana sai Malamai sun zama masu kwadayi da karya da yaudara sannan al'umma take lalacewa. Abin daya faru kwanan nan ga 'yar uwata musulma MARYAM USMAN HIYANA ba kowa ya bada kofar faruwar hakan ba face malamai domin su ne basu yi aikin da Allah SWT ya dora musu ba saboda tsoron dauri da talauci. Lalle da Malamai sun fadakar sun tsoratar da al'umma tun farkon bayyanar Fim din SANGAYA wanda shine ya jawo matasa maza da mata suka bazama neman shiga harkar Fim don su ma duniya ta san su, su yi suna, su nuna irin halittar da Allah SWT yayi musu ga masu bukata, da wancan al'amarin rashin jin dadi bai faru ga waccan matata ba.
Ina son masu karatu da wanda suka kira ni a waya su sani cewa ni bana tsoron mutuwa akan gaskiya domin ita mutuwa dole ce, wani ma ya yadda ya mutu a hanyar kafirci bare ni da nake kira a bi hanyar gaskiya hanyar Allah SWT. Bana kaunar abin da Malaman mu suka jawo mana na kaskanci wanda yayi sanadin 'yan mata musulmi suka gwammace shiga harkar fina-finan hausa maimakon yin aure wanda shine yafi mutunci a gare su da mu kan mu. Malamai da kun jefar da al'adar kafirta musulmi mai salla da azumi da zikirin Allah SWT kun bi hanyar da Muhammadu Dan Abdullahi, Baban Sayyada Fatima, Yayan Aliyu Dan Abi Dalib, Kakan Hassan da Hussain da Shehu Tijjani da Sidi Abdulkadir Jilani, tsiran Allah da albarka su kara tabbata ga shugabana Muhammad da Iyalansa masu tsarki, wallahi Allah da babu wata yarinya baliga musulma,ko wadda ma ba musulmar ba,da zata shigo garin Kano da sunan a bata suturar fitsaranci,domin ta bayyana surarta,a sanya mata waka da kida tana rawa,mai camera yana daukar hotonta da sunan sana'a,kuma har akai wannan abu gaban jami'an gwamnatin musulunci ta jihar Kano su amince da wannan abu ya shiga kasuwa da izinin gwamnatin musulunci ta jihar Kano, a halin akwai malamai a cikin hukumar da data bada izinin shigar da wannan kaset kasuwa. Haba al'ummar Muhammadur Rasulillah SAWA muji tsoron Allah SWT mu daina yaudarar kawunanmu da sunan addini, idan zamu yi musulunci muyi shi gaba daya kada muyi imani da wani bangare mu kafirce da wani bangare, idan mun yi haka uwarmu daya ubanmu daya da Bush mai antaya bama-bamai akan al'ummar Manzon Allah SAWA jarirai da yara, mata da tsofaffi a kasashen Iraki da Afganistan, kuma ina son in tunatar da ku Allah SWT ya la'anci Yahudu ne saboda Malamansu suna sauya hukuncin daya saukar musu kamar yadda malamanmu a yau suke halasta zalunci da fajirci matukar dai za a basu kujerun hajji da kwangiloli da 'yan milliyoyin Nairori.
A karshe ina kira ga al'ummar hausa Fulani da kabilun cikinmu wadanda suka dauki sana'ar fim din hausa sana'a a garesu da su rike wannan sana'ata su da hannu biyu kuma su sanya tsoron Allah SWT a cikin wannan sana'a tasu domin sana'a ce wadda zata kai su ga samun rahamar Allah SWT matukar sun riketa tsakaninsu da Allah SWT da nufin illimantar da al'umma addinin Allah SWT da kuma nusar da al'umma kyawawan dabi'un musulunci da kuma munanan dabi'u. Hakan zai tabbatu kawai ne idan masu wannan harka ta fina-finai sun ji tsoron Allah SWT kuma sun nemi illimi na wannan sana'a tasu a addinance sun san abin da musulunci ya amince suyi a wannan sana'a tasu da kuma abin da yake haramun kuma suka yi hakan da kyakkyawar niyya. Sannan matan da suke baro kyauyukansu da rigagensu da biranensu suke kwararowa garin Kano da sunan sun zo shiga harkar fina-finan hausa wannan ya dace ya zama tarihi, domin babu ta yadda musulunci zai yadda da wannan abu. Kuma wannan abu ne ya jawo 'yan mata 'yan fim suka mai da karuwanci sana'a domin basa gaban iyayensu kuma basa gaban muharramansu, dama sun zo Kano ne neman kudi. Wanda da ace a lokacin da suka zo garin Kano sun samu Malamai sun yi aikin daya rataya akansu da babu wanda zai sauke su bare ya basu masauki a shagonsa ko a gidan gwaurantarsa ya fake da cewa sana'a suka zo yi. Kuma Ibrahim Mandawari kana cikin wanda ya ingiza mata 'yan fim fadawa cikin muguwar hanya musamman ta hanyar shirinka na Fina-finan hausa da kake gabatarwa a gidan rediyon Freedom,a cikinsa kake fito da matakai na arziki da masu sana'ar fina-finai na hausa suke takawa wanda da kunne na naji kana lissafin matan da suka mallaki mota a hanyar fim, wanda hakan kana bude kofa ne ga mata su baro gidajen iyayensu ko auransu su fada harkar fim, wanda sai sun fada harkar sai su ga abin ba haka bane ba, idan suna son mallakar mota sai sun bi ta hannun kawalai sun hada su da fasikai. Kuma ina fatan Ibrahim Mandawari ba zaka manta da abin da ka fada kai da 'yan uwanka masu fim a ranar lahadin da ka gabatar da shirin "Dan Kuka Mai Jawo Uwarsa..." wanda kayi akan abin rashin dadin daya faru na Maryam Hiyana a gidan rediyon Freedom inda da bakinka kai da sauran 'yan fim da ka gayyato kuka ce babu ta yanda za ayi mace ta mallaki mota a sana'ar fim a halin irinsu na Kwango da Sule Koki basu mallaka ba idan dai har da kudin da ake biyan ta ne.
A karshe Malamai dana batawa rai akan abin dana fada na gaskiya bana bukatar su yi hakuri, bukata ta kawai shine su bi hanyar shiriya su tserar da al'umma. Sannan 'yan fim din hausa musamman mata kar ku dauka ina mara muku baya ne, a'a, ni ina fadar gaskiya ne wadda ko ta kare ce ya dace a bashi kayarsa. Ni bana goyon bayan waka da rawa da muguwar shiga da kuke yi a fina-finan hausa, domin wannan ya sabawa addini na da al'ada ta, kuma ina bakin ciki da halin da malamai suka jefa ku a ciki har kuka samu kan ku a cikin wannan muguwar hanya, domin da malamai sun illimantar da al'umma kuma sun wa'azantar da al'umma da baku samu kanku a wannan muguwar hanya ba, Allah ya saka muku a bisa zaluncin da malamai suka yi muku, suka bar ku kuka fada muguwar hanya wanda da sun yi aiki da illiminsu wallahi da dukkan ku kuna gidajen mazajenku kuna cin ribar rayuwarku ta hanyar kyautatawa mazajen ku, ku sanya musu kananan kaya a baku lada, ku musu girki mai dadi a baku lada, ku yi hira dasu a baku lada, ku yi musu magana mai dadi a baku lada. Amma gashi sun zalunce ku sun barku cikin kaskanci da shaye shaye da muguwar makoma a gobe kiyama.
DAGA:
RABIU HAMDALA KANO,
08065273401.

No comments: