6.12.07

Hana rawar batsa da wakar fajirci da hukumomi a jihata ta Kano suka yi a cikin fina-finan hausa wannan wani yunkuri ne wanda ya zama dole na mikewa tsaye kuma na cirewa hula, sannan na hade hannayena na yiwa tafi, raf! raf! raf!

Babu wani bahaushe musulmi mai salla, mai cikakken hankali da zai amince da irin abin da aka aikata a cikin wakar 'BABBAR RIGA' wadda akayi a fim din Babbar Riga kuma ya amince da cewa wannan waka tayi daidai da addinin mutanen Kano, ko da al'adarsu, wanda wannan waka ita kadai ta isa ta bude kofofin masifu ga al'ummar mutanen Kano domin babu abin da aka nuna a cikin wannan waka face tsantsar fajirci da wulakanta bahaushe da mai dashi wawa mara tunani mara kishin al'ummarsa. Idan ba haka ba ta yaya zai zuba ido wasu banza bakwai su zo har garinsa, su shiga rigarsa, su dauki yaransa su wulakanta shi a idon duniya da sunan nishadantarwa. Dubi yadda aka yi amfani da al'adun bahaushe a wannan wakar, ka ga dai sarautarsa, rawaninsa, fadarsa, rigar mutuncinsa kuma aka zo aka hada da al'adar da bata da tushe hatta a wajen wadanda aka kwaikwaya domin shigar da matan da aka yi wannan waka dasu ko a turawan ma sai tatacciyar 'yar...................... ce zata yi wannan shiga, amma sai gashi a na bayyana wadannan 'yan mata a matsayin hausawa. Shin wannan fim mai dauke da wannan muguwar waka dama ya bi ta hukumar AA Kurawa kuma malaman hukumar sun ga wannan waka kuma suka barta ta shiga kasuwa tun a lokacin?

Bani da wani gilli akan wanda ya shirya wancan fim face dai na san ya wukalanta mini al'adata a matsayinsa na wanda ban taba damuwa da al'adarsa ba ko kabilarsa ba duk dana san suna da miyagun dabi'un da zan iya shirya fim akansu domin daukarwa al'ummata fansa akai amma ni bana jin zan aikata haka