8.4.10

Ina mamakin yadda al'ummar hausawa zata kasance nan da wasu shekaru masu zuwa, kasancewar yadda na ga illimin addini yawaita a tsakanin al'ummar hausawa, ko'ina ka duba sai kaga sabuwar makarantar islamiyya, a zauren gida ne, a cikin gidan matan aure ne har da kofar gidaje a yau zaka ga ana karatun addini. Sannan babu unguwar da zaka shiga a cikin birnin Kano da kewayenta baka ga duk kwararon da ka shiga ko lungu baka ga masallaci akalla guda biyu ba ko da kuwa irin mazaunar nan ce ta hirar samari ko ta 'yan boko da suke haduwa suyi salla. Massalatan Jumma'a kuwa abin kamar bizines nan kaji ana salla karfe daya can kaji daya da rabi suke salla, can kuma karfe biyu ake salla.

Duk da irin wancan cigaban addinin da aka samu a kasar Hausa wanda ba zan ce uffan akai ba, sai gashi mun fi kowa tozarta al'amarin aure da sakaci da tarbiyar 'ya'yanmu wadanda sune jarinmu mafi tsada kuma sune abin alfaharinmu, muna raye ne ko kuwa muna a mace ne. Sannan yana yin neman aurenmu da zamantakewar aurenmu mu da yadda muke tarbiyar 'ya'yanmu mu hausawa a yau tayi nesa da yadda addininmu ya tsara mana mu bi, amma idan an zo maganar addini mun fi kowa daukar zafi a halin gashi mun yiwa addininmu tsira a kasuwa.

A yau duk kasar Najeriya babu wata kabila da take kaunar ta baiwa Malam bahaushe aure saboda yadda ya zama lamba daya wajen tozarta aure. A jaridar Aminiya an taba bada labarin wani mutum mai suna Ali dan kabilar babur daya kashe 'yar sa a dalilin zata auri bahaushe. Yanzu wannan kadai bai isa ya nunawa duniya yadda muka yi watsi da kyawawar al'adar nan ta mu ta rikon aure da tarbiyar 'ya'yanmu ba. A yau a jihata ta Kano sakin aure da zinace-zainace da suke aukuwa tsakanin ofisoshin gwamnati da ma'aikatu da dakunan otal-otal da kuma gidaje a kullum yafi yawan haihuwa da ake yi a kullum! Da wannan irin muguwar dabi'a ce muke tunanin samun zuriya ta gari?