12.11.07

YAN FIM SUN FI MALAMAI

Edita ina muku sallama ta addinin musulunci ke da abokan aiki da masu karatu, wato, Assalama alaikum.
Bayan haka edita na karanta hirar Ibro da kuka buga a mujallar Fim mai farin jini inda har Ibro yake cewa sun fi Malamai fadakarwa su 'yan Fim, wannan magana ta Ibro haka take babu ja domin Ibro ya fadi wannan magana ne bisa sani ba wai bisa son zuciyarsa ba.
Abin daya sa na fadi haka kuwa har nake jinjina ga shi Ibro shi ne da farko dai shi Ibro yana nufin "Ulama'u Suki" wato Malamai masu harkar kasuwanci da ayoyin alkur'ani wadanda suke raba kan al'ummar musulmi ta hanyar kungiyoyinsu mara sa amfani ga addini. Malamai wadanda suke rabon kaulasan wato suke kafirta mutanen da suka shaida babu wani abin bautawa da gaskiya sai Allah (swt) kuma Muhammadu (sawa) Manzon Allah ne, sannan suka tsaida salla suke kuma bada zakka, wanda Manzon Allah (sawa) ya ce duk wanda ya aikata haka mutuncinsa da jininsa ya kubuta al'amarinsa yana hannun Allah. Amma irin wadancan malamai suka ce ba haka ba, domin kuwa da sun yarda da haka da sun tsaya akan wannan magana ta Manzon Allah (sawa) domin kuwa Allah (swt) da kansa yake fadin duk mutumin da yayi imani da Allah (swt) yake kuma fatan ya hadu da Allah lafiya a gobe kiyama to abin koyinsa shine Annabi Muhammadu (sawa). Shin yanzu irin wadancan malamai da suke kafirta musulmi mai salla mai taimakawa 'yan uwansa da dukiyarsa da wa suke koyi kenan? Domin Manzon Allah (sawa) bai cutar da larabawa ba wadanda ya tarar dasu sun fi kowa kafirci a duniya a lokacin bayyanarsa, domin ya samu larabawa suna binne 'ya'yansu mata da ransu, kuma suna kwace da fashin dukiyoyin jama'a tare da sanya mataye rawa tsirara da sunan bauta, ruwan giya kuwa shi ne ruwan shan su mushe kuwa abin kalacin su, karuwai kuwa har tuta suke sawa a samun dakunansu, sannan uwa uba gumaka dari uku da wani abu ne a dakin Ka'aba da su larabawa suke bautawa, amma Manzon Allah (sawa) dan Abdullahi mai kira abi Allah (swt) wanda karya bata hada hanya da shi, Allah (swt) ya tashe shi a cikinsu ya kuma kira su zuwa ga hanyar Allah (swt) ta hanyar kira mai cike da girmama dan Adam ba tozarta shi ba ko wulakanta shi ba, wanda hakan ya sanya hatta manyan kafiran Makka suna kiran Manzon Rahama (sawa) da Al-amin wato mai gaskiya da amana.
Da Malamanmu sun tsaya akan koyarwar Manzon Allah (sawa) sun watsar da baiwa mata rubutu su wanke gabansu dashi, sun watsar da yiwa matan aure ciki a makarantun Islamiyyoyi, sun watsar da yin sihiri da ayoyin alkur'ani mai girma suna raba uba da dansa, uwa da danta, suna sanya gaba tsakanin miji da matarsa, sun daina bi ofisoshin gwamnati ana basu na kalaci, sun daina baiwa 'yan siyasa layu suna kwana tsirara a makabartu, sun dawo akan hanyar gaskiya hanyar kira zuwa ga Allah (swt) ba hanyar tara mutane ba su sanya su a hanyar siyasar dimokaradiyyar Amurka bayan sun sace musu imaninsu, to wallahi da babu wani ko wata yarinya da zata baro kauyansu ta shigo garin Kano da sunan a sanya mata abin daukar hoton bidiyo tana karya kwankwaso ita da namiji baligi da sunan neman abinci. Wanda masu yin hakan dama su sun sallama kansu a matsayin fitsararu masu kangarewa Allah (swt) da Manzonsa (sawa) domin su basu kira kansu masu bin tafarki ba, wanda ko a lahira wutar mai munafunci da wasa da izgilanci da cin abinci da ayoyin Allah (swt) ta fi ta wanda yake aikata sabonsa da rashin sani ko jahilci.
Ina so mutane su yi adalci kuma su bude kwakwalensu su fadi gaskiya a tsakaninsu da Allah (swt) su duba su gani da 'Yan Fim da malamai su waye suka fi fadakar da al'umma mu dauke son zuciya mu fadi gaskiya domin gaskiya ko ta kare ce ka bashi kayansa. Mu duba muga irin bala'in da kaskancin da muke ciki a yau su waye suka jawo mana "yan fim ko Malamai? Idan baku sani ba to ga tambaya su waye suke halasta aure akan aure? Su waye suke gyaran aure saki? Su waye suke cewa dan kungiya kaza kafiri ne? Su waye suke karbar kudin daurin aure idan suka kulla aure? Su waye suke cin dukiyoyin marayu a gidajen mutuwa da sunan suna yiwa mamatansu addu'a? Su waye suke boye ma'anonin gaskiya na ayoyin Allah (swt) su sanya son zukatansu? Su waye suke suke siyasar dimokaradiyya da addini a halin sun san ba a dora ginshikin gini akan iska? To amsar idan baku sani kuce Malamai masu ciniki da ayoyin Allah (swt) wandanda suke kirkirar karya su jingina ga Allah (swt).
Idan dan Fim yana aikata daya daga cikin wadancan abubuwa dana fada ku fada mini. Kuma idan dan fim ya taba fitowa yace shi na Allah ne ku zo ya wuce muku gaba ku fada mini?
A yau ta hanyar sana'ar Fim din Hausa wadda take da cibiya a Kano mutane da yawan gaske sun iya warware matsalolin zamantakewar su da matansu da 'ya'yansu da iyayensu da makwabtansu kai har ma da wadanda ba addininmu daya dasu ba wannan sana'a ta Fim din Hausa ta wayarwa da jama'a da yawan gaske kai, inda zaka ga mace ta koyi yadda zata yiwa mijinta magana cikin ladabi, wata kuma ta koyi yadda zata zauna da iyayen mijinta da 'yan uwansa, wata kuwa ta hanyar Fim din Hausa ta fahimci dalilin da mijinta yake dadewa a hirar dare ta kuma gyara kuskurenta cikin sauki. Ba wai mata kawai ne ba suka fa'idantu da wa'azantarwa da suke cikin Fina-finan Hausa ba har ma da mu maza wanda muke aikata miyagun ayyuka mun ga karshen yadda masu neman 'yan mata yake zuwa musu da nadama, mun ga karshen masu kin taimakawa dangin su da 'yan uwansu duk masu Fina-finan Hausa din nan sun nuna mana ta hanyar sana'arsu kuma ya kasance darasi da wa'azi agaremu domin idan bai faru da kai ba to ya faru ga wani ka gani.
Mu koma ga Littafin da ya fi kowane littafi muhimmanci da daraja da girma wato alkur'ani mai girma wanda da shine muke fahimtar addini kuma shine littafin daya tattara kome da komai na illimi, wanda ina ji fiye da kashi biyar cikin goma na alkur'ani mai girma labarai ne na mutane da alkaryu iri-iri da suka gabata Allah yake bamu domin mu shiga taitayinmu wanda duk mai imani idan ana karanta masa alkur'ani kasancewa yake yi tamkar ana nuna masa abin ne a cikin zuciyarsa. Sannan duk irin kirkinki ka idan kana karanta alkur'ani zaka ji labarin wanda ya fi ka nagarta da kirki haka nan duk iya shegenka zaka ji wanda ya fi ka kuma kaji yadda Allah (swt) mai kowa mai kome yayi da shi, wanda ta haka za ka zabawa kanka inda kake son shiga a gobe kiyama. Haka nan ma suma ma masu Fina-finan Hausa labari ne suke badawa wanda a karshe zaka ga makomar wanda aka gina labarin akan sa idan azzalumi ne zaka gani, idan mutumin kirki ne shima zaka gani karshensa. Inda cikin hikima suka dunkule maka rayuwa a cikin awa biyu ko kasa da haka kuma suka sanar da kai yadda take wanda duk jahilcinka dole ne ka fahimci abin da ake nufi domin dai da yarenka aka shirya Fim din konace wa'azin. Ko bamu ga yadda abokan zamanmu suke yada manufofin addinin su ba ta hanyar fina-finan su ba, wanda kuma yake samun tasirin gaske a tsakaninsu
Sannan kuma akwai bambamci tsakanin wa'azin malaman zamani da wa'azin masu fina-finan zamani da farko dai mai wa'azin zamani duk mutumin da fahimtarsa ta saba da tasa a wajensa idan yayi masa da sauki ya kira shi kafiri. Sannan kuma mai wa'azin zamani kome ya sani, baya tunawa da cewa kome kake akai akwai sama da kai idan ba haka ba ta yaya zai kira mai yawaita fadin kalmar La'ilaha illallah Muhammadur Rasulillah, mai yawan salatin Manzon Allah (sawa) kuma mai yawan tuba izuwa ga Allah (swt) kafiri saboda yayi imani da abin da yake yi. Wanda babu wani dan Fim ko ince mai shirin fina-finan hausa da zai yi haka a hanyar fina-finansa. Kuma duk tsiyar mai shirin Fina-finan Hausa ba za ka taba jin ya sauya fassara littafin Allah (swt) ba domin ya biyawa wani bukatar sa ba, shi dai ka bar shi akan sana'arsa ta Fina-finan Hausa kawai wadda jama'a suke amfana da kokarinsa ko ince wa'azinsa. Karshen mai tabara da iskanci a wasan Hausa ba sama da Ibro, amma ban taba jin an kira sunan Manzon Allah (sawa) ba a cikin wasan Ibro ba tare da Ibro yayi salati ga Manzon Allah (sawa) ba, kuma naga mutumin daya haddace hadisan Manzon Allah (sawa) masu yawa ta hanyar Fina-finan Ibro wanda Malam Dare yake kawowa a duk Fim din Ibro.
Sannan mai shirin fim idan dan iska ne masu kallo sun sani domin shigarsa da kalmar bakinsa ta isa su yi masa hukunci domin babu munafunci a tare da shi, ya rage na mai kallo ya san na dauka yasan na jefarwa. Amma malamin da zai fada maka Allah a bakinsa amma a zuciyarsa babu Allah kuma idan ya ganka baka san inda aka dosa ba sai yayi ta wasa da kwakwalwarka, har wata rana kaji mutum yana kiran kansa shi Allah ne an bashi wuridi ya samu motsuwa, Allah ka tsare mu! Amma dan Fim iyakaci ya mai da kai mai rawa a cikin jama'a idan ka dauki hanyar fitsararun masu fim kenan, ko su mai da ke mai yawo tsirara a gari ta hanyar sa suturar banza idan baki san mutuncin kanki ba. Amma karya ne mutum yace ya koyi shaye-shaye ta hanyar fim din Hausa ko ya koyi munafunci ta hanyar fim din Hausa ko ya koyi kafirta dan uwansa musulmi ta hanyar fim din hausa.
A karshe ina kira da mutanen da suka jahilci maganar Ibro da yace su masu fim sun fi Malamai fadakarwa su fahimci abin da Ibro yake nufi kuma su yi masa adalci wajen yi masa kyakkyawar fahimta. Sannan kuma su lura da cewa sai Malamai sun bar koyarwar Manzon Rahama (sawa) ne al'umma take fadawa cikin bala'i da masifu iri-iri domin aikin da masu fim din hausa suke yi aiki ne na malamai wanda suka watsar suka kama business da addini sai da azumi su kama aikin da ya dace ace a tsawon shekara shi suke yi. Mu duba mu gani a garin Kano musamman gidajen Malamai masu kafirta al'umma zamu ga duk abin da tattaciyar mara kunyar 'yar fim take yi shi suma 'ya'yansu daya dace su zama abin koyi suke aikatawa, ku je jami'o'i da makarantu ku gani.
Malamai ku ji tsoron Allah (swt) ku daina kwadayi ku tsaya kyam akan tafarkin Allah (swt) domin ku ne kuka lalace shi yasa matasanmu suka nemawa kansu hanyoyin da suke ganin sune mafita a tare da su a halin kuwa hanyoyin halaka ne suka fada. Tabbas al'umma zata gyaru idan har Malamai suka yi aiki tsakani da Allah (swt) hatta fina-finan nan da 'yan Jos da Kaduna suke ta kwararowa jihar Kano suke abin da suka koya a gidajensu wanda su a tarbiyyarsu haka shine daidai idan Malamai na Allah suka shiga wannan harka fina-finai lalle za su tsarkake harkar kuma wannan zai rage musu aiki wajen isar da Sakon Allah (swt) ga 'yan uwanmu na kasa daya wadanda har yanzu ba a samu masu kai musu addinin Allah (swt) ba ta hanyar da zasu fahimce shi ba wanda a kullum burinmu mu kira su da miyagun sunaye na arna ko muce da su arnaku wanda abin da suke na sabo da kannenmu suke yi ko yayyenmu ko mu da kanmu, suturar da matar da ba musulma ba kuma tattaciyar 'yar banza a cikin wadanda ba musulmin zata sanya ita 'yar musulmi ayau take sanyawa, ayau 'ya'yan musulmi sune masu layi a gidajen shan giya inda zaka ga wanda ba musulmi ba ya sha kwalba daya ya hakura amma sai kaga dan musulmi ya sha katan guda ya kara madarar sukudaye ko wiwi, haka 'ya'yan wadanda ba musulmi ba ayau sune 'ya'yan musulmi suke zinace zinace da su kuma idan magana ta tashi sai muce musu arna a halin abin da suke aikatawa shi 'ya'yan musulmi suke aikatawa.
kirana na karshe ga shugabannin masu harkar fina-finan Hausa na Kano wanda daga masu kiran kansu jikokin Manzon Allah (sawa) sai wanda suke 'ya'yan malamai da Manyan limamai da sauransu da su yiwa Allah da Manzonsa su kawo gyara a cikin wannan sana'a tasu wadda da ita za su iya jihadi mai fadin gaske da ita fiye da dukkan wani abu da wani Malami zai yi a wannan lokaci, domin mata da yara da manya dukkansu suna kaunarsu tare da basu lokutansu wajen sauraran abin da suke kokarin isarwa.
RABIU HAMDALA

No comments: