12.11.07

BOBO-HIYANA

salam.

Yan uwana musulmi ina muku barka da warhaka. Naga labarin abin daya faru na hoton bidiyon tsiraici na 'Yar wasan Hausa Maryama Hiyana wanda jaridar almizan ta buga. Lalle almizan nayi mamakin yadda kika bayyana Ibrahim Mandawari a matsayin wani mutumin kirki a halin shine wanda yayi sanadin fadawar wannan yarinya cikin wannan harka ta fitsara wadda ake koyawa yara mata da sunan sana'ar Fina-finan hausa. Abin daya sa na fadi haka kuwa shine, shi dai wancan mutumi, Ibrahim Mandawari shine wanda ya fari waka a cikin Fim din hausa, a wani wasa mai suna Jamila da jamilu wanda daga nan ya bude kofofin wakokin fina-finai wanda a sakamakon haka ya yaudadrar da tunanin matasa masoya Manzon Allah SAWA wadanda suke nishadantar da kuma illimantar da al'umma cikin yabon da suke yi wa shugaban halitta Manzo Muhammad SAWA, wanda saboda akasarin matasan basu samu tarbiyyar ruhi ta gaskiya ba sai suka fada cikin wakokin hausa na soyayya saboda kudaden da suka hangen samu a wannan sabuwar hanya wadda tayi hannun riga da tarbiyyar musulunci, kuma tayi daidai da tarbiyya da al'ada ta masu bautar gumakan Kirishna da Budha dake kasar Indiya, kuma suka dauki salon raye-rayensu da suke yi tsakanin mata da maza wanda ko mahaukaci ya san ya sabawa hanyar tarbiyyar musulunci, amma malamanmu na fada dana zaure dana talabijin da rediyo da shehunanmu duk suka zuba ido suna gani saboda domin su kullum suna hangen abin da ya faru a baya ne ko kuma ake ciki basa hangen gobe kiyama da abin da zai kassance a gobe a gidan duniyar da muke ciki ba.
A shekearun da suka gabata idan ka ji muryar budurwa tana rera wake ka tabbata yabon Manzon Allah SAWA ne da Iyalansa ko sahabbansa, kuma duk wadda ta kware wajen rera yabon Manzon Allah SAWA zaka gani duk muninta rububin aurenta jama'a suke yi domin tayi riko da igiyar da bata rubewa bare ta tsinke, kuma duk zinar mazinaci ba zai yi sha'awar yin lalata da ita ba, domin duk abin da mutum yake so yana tare da shi, masu yabon Manzon Allah SAWA suna tare da Manzon Allah SAWA kuma suna cikin kariyarsa a duniya da lahira. Jama'a ku dubi Shareef Rabiu Usman Baba, ku dubi Mustapha Gadon Kaya, ku dubi Malam Hussain na Shehu Aliyu Harazimi Kano, Ku dubi Hassan Alaye da Bashir Dandago wanda wata yarinya tayi mafarki da Nana Fatima As inda ta fada mata tayiwa Malam Bashir Dandago albishir da gidan aljanna.
Kishiyar wancan zancen nawa sune masu wakokin Fina-finan batsa na Hausa inda zaka ga ana kalaman da ko mahaukaci ya san batsane a cikinsu wanda zaka ji wasu wakokin fitsarane kai tsaye misalinsu sun hada irinsu, "ZUBAR GADO ! wadda Yakubu Mohammed yayi da wakar Shaba, "YI MATA RAWA" da wakar , JAMILA TA IYA DAURA ZANI da wakar BABBAR RIGA wanda Sani Danja yayi su. Zaku amince dani idan kuka ji furucin da wannan mawaka suke yi a cikin wakokinsu wanda kuma ake musu shiga wadda tayi daidai da sakon da suke isarwa zuwa ga al'umma, kuma a cikin irin wannan wakokin ne matan 'yan Fim din batsa na Hausa suke tallan kansu ga masu bukata ta hanyar yin duk wani abun da zai isar da sakon zuciya ga dangin jama'ar Annabi Lud As da muke zaune dasu a wannan kasa. Kuma akasarin masu neman matan nan suna amfani da wayoyin masu sanya su aikata wannan aikin masha'a ne da ake kiransu Darektos wanda suke sanya lambobin wayoyinsu a jikin bangon kwalin kaset din suka yi, wanda tana nan ne mai bukata zai kulla ciniki da su.
Babu wani mai laifin daya wuce Malam Ibrahim Shekarau a cikin abin da masu Fina-finan hausa suke aikatawa a jihar Kano, domin shine jagoran jihar kuma duk abin daya ke faruwa a jiharsa yana sane da shi, wanda har kyaututtuka yake rabawa 'yan wasan hausa a halin yana sane da irin abin da suke gudanarwa a ciki da wajen jiharsa, kuma hukumar daya kafa ta tace fina-finai wadda take dauke da wasu mutane da ake kira Malamai magada arnan baya wanda sune suke baiwa kowane fim damar fitowa kasuwa idan sun duba shi kuma wai suka tabbatar ya dace da tsarin koyarwar addinin musulunci, ko wadannan magada arnan baya suna ina ne a lokacin da Fim din GUDA ya fito? Kuma suna ina ne Sani Danja ya fitar da Fim dinsa na MAI BABBAR RIGA ? Tabbas lokaci yayi da al'umma zata zabawa kanta mafita ko dai ta bi hanyar Allah SWT wadda yake fawwalawa wasu daga bayinsa wadanda ya zaba su bayyanawa mutane mafita ko kuma su hadu da mutanen Fir'auna da Abu jahil a matattara guda.
Naji ance gwamnatin Kano wai ta dakatar yin Fina-finan batsa na hausa har tsawon shekara guda, amma gidajen rediyo mallakarta suna nan suna dada tallan wadannan fina-finan batsa na hausa ta hanyar sanya wakokin batsar da suka yi a baya. Shin jagoran Gwamnatin jihar Kano bai san da yunkurin da almajiran Malamin nan na Zariya suka yi ba na yin Fim din Shehu Usman Dan Fodio ba ne ba? Idan ya sani wace irin gudumowa ya bada a matsayinsa na wanda ya amfani jihadin Shehu? Mu ma 'Yan Tijjaniyya muna binsa bashi domin muna da hakkin ya sa ayi mana Fim din Shehu Tijjani domin Malamanmu sun tare a gidansa suna kwadayin abin duniya, har suna zuga shi wai 'Yan Kadiriyya sun zama Shi'a.
Shawarata ga babban yayana Malam Ibrahim Shekarau itace ya ruguza harkar Fina-finan batsa na hausa har abada, kuma ya hana wakokin soyayya irin nasu har abada, sannan ya nemi mutane masana addini su kirkiri wani abu wanda zai maye waccan muguwar sana'a irinta mutanen Annabi Ludu, kuma ya hana shirin da Ibrahim Mandawari yake gabatarwa a gidan rediyon Freedom dake Kano na Fina-Finan hausa wanda yake taimakawa wajen yada wancan fasadi, kuma yayiwa Allah da Manzonsa ya kai ziyara Sokoto domin sulhunta al'ummar musulmi ya taimaki masu gaskiya ya kuma yiwa marasa gaskiya fada ya kuma taimaki wadanda aka konewa dukiya da gidaje domin shi dai na Allah ne, kuma saboda haka jama'a suka zabe shi domin kullum yana fadin Allah.
RABIU YUSUF
08065273401

No comments: